Sanata Dino Malaye ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne yafi kowa cancantar zama shugaban kasan Najeriya.
Dino malaya ya bayyana hakan ne a wani bideyo daya saki a shafinsa na Twitter ranar juma’a.
Inda yace Atiku ya auri gabadaya manyan kabilun kasar nan, watau Hausa, Yoruba da kuma Igbo.
Saboda haka yanzu lokacin sane ya jagoranci kasar ne don zai nagance matsalar kabilanci, amma shi Obi yayi hakuri ba zai zama shugaban kasa yanzu ba.