fbpx
Friday, July 1
Shadow

Attajirin Duniya, Jeff Bozes ya samu habakar arziki ta Dala Biliyan 13 a rana daya

Attajirin Duniya, me kamfanin Amazon, Jeff Bozes dake sayar da kaya ta yanar gizo ya samu habakar Arziki a jiya Litinin kawai ta Dala Biliyab 13.

 

Kafar dake kula da kawo labaran tattalin arziki ta Bloomberg ta bayyana cewa wannan kudi sune na farko da aka taba samun wani dan kasuwa ya samesu a rana daya tun sanda ta fara saka ido akan harkokin masu kudin Duniya.

Bozes dan shekaru 56 wanda shine mutum na 1 a Duniya wajan Arziki ya samu habakar dukiyarsa daga Biliyan 74 zuwa Biliyan 189 a shekarar 2020 duk da zuwan annobar cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Matarsa kuwa da suka rabu, Mackenzie Bozes ta samu Dala Biliyan 4.6 wanda hakan ya bata damar zama mutum ta 13 data fi kowa Arziki a Duniya.

 

Masana sun bayyana wannan habakar arziki da zaman gida da aka yi dalilin zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 da kuma yanda kasar Amurka ta baiwa ‘yan kasarta Tallafin kudi dan su kula da kansu.

 

Koda me kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg ya samu habakar tattalin arziki da ya kai Dala biliyan 15.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.