Tauraruwar fina-finan Hausa,Rahama Sadau ta bayyana cewa yin aure ba zai sa ta daina sana’arta ta fim ba.
Ta bayyana hakane a matsayin amsa ga wani da ya tambayeta shin idan ta ti aure zata daina yin fim?
Rahama tace wane dalili zai sa ta daina yin fim? Tace akwai sana’o’i da ayyuka da dama da mata ke yi wanda basa dainawa idan sun yi aure, misali aikin jarida. Tace itama harkar Fim sana’a ce.
Rahama ta baiwa Masoyanta damar yi mata tambayoyine a shafinta na Twitter inda a nan ne ta bayar da wannan amsa.
Ta kuma bayyana cewa, yanzu haka tana soyayya da wani kuma har soyayyar ta yi karfi sosau.
Rahama ya kuma bayyana cewa itana tana so ta kawo wasu ta Raine su a masana’antar Kannywood kamar yanda Ali Nuhu ya mata.
Why quit filmmaking for marriage? Is filmmaking not an occupation? Why is it okay to have women in different areas of organization but not in filmmaking ? Media for example🤔 #AskRahama https://t.co/DnSBya3xH6
— Rahama Sadau 🇳🇬 (@Rahma_sadau) January 6, 2021
Why quit filmmaking for marriage? Is filmmaking not an occupation? Why is it okay to have women in different areas of organization but not in filmmaking ? Media for example🤔 #AskRahama
Yes. I’m on the verge of doing that. In shaa Allah #AskRahama ✌🏻🌟 https://t.co/D8WHWG9wPu
— Rahama Sadau 🇳🇬 (@Rahma_sadau) January 6, 2021
Insecurity 😭😩 #AskRahama https://t.co/Ikleq8V6bk
— Rahama Sadau 🇳🇬 (@Rahma_sadau) January 6, 2021