fbpx
Monday, December 5
Shadow

Author: Musa Abdullahi

DA DUMI-DUMI: ‘Yan bindiga sun kona ofishin INEC a Enugu

DA DUMI-DUMI: ‘Yan bindiga sun kona ofishin INEC a Enugu

Breaking News
Wasu da ba a san ko su waye ba sun kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta karamar hukumar Igboeze ta Arewa a jihar Enugu. Ofishin da ke hedikwatar majalisar a Ogurute ya kone kurmus a daren Lahadi kuma ginin da abin ya shafa ya kone gaba daya. An tattaro cewa hukumar kashe gobara ta jihar da ke da ofishi a Ogurute ta kasa shiga domin kashe gobarar saboda fargabar sake kai hare-hare har sai da aka samar da jami'an tsaro, yayin da kafin isowarsu ofishin ya kone kurmus. Cikakken rahoto yana nan tafe....
Yajin aikin Kungiyar ASUU ya tilasta min farautar mijin aure cikin gaggawa – Wata dalibar ‘yar shekara 20 ta koka

Yajin aikin Kungiyar ASUU ya tilasta min farautar mijin aure cikin gaggawa – Wata dalibar ‘yar shekara 20 ta koka

Breaking News
Wata yarinya ‘yar shekara 20 da haihuwa kuma dalibar jami’ar jihar Gombe (GSU) mai suna Maryam Adamu, ta koka da yadda kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yajin aiki wanda tilasta mata neman mijin aure cikin gaggawa. Dalibar jami’ar GSU mai matakin karatu 200, ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da manema labarai a Gombe, inda ta ce yajin aikin ya ruguza shirinta da burinta kammala karatunta tun kafin ta kai shekara 20 da kuma burin yin aure bayan ta kammala karatunta. Dalibar ta kara da cewa; ASUU da gwamnati za su iya ci gaba da wasansu domin kuwa a halin yanzu auren ne ke gabanta.
Yan sanda sun kama wasu mutane 7 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne tare da kwato makamai a Jihar Edo

Yan sanda sun kama wasu mutane 7 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne tare da kwato makamai a Jihar Edo

Laifuka
Rundunar ‘yan sandan jihar Edo a ranar Lahadi ta ce jami’anta sun kama wasu mutane bakwai da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne a jihar. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakiyar jami’in hulda da jama’a, ASP Jennifer Iwegbu, wacce aka rabawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Benin. NAN ta tuna cewa rundunar ‘yan sanda a ranar Juma’a ta kama tare da gabatar da ‘yan kungiyar asiri bakwai, wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne na Eiye da Aiye. Iwegbu ta bayyana sunayen wadanda ake zargin Andrew Owhoyavwosa mai shekaru 22 da Joseph Meshak 25 da Osazee Solomon 35 da Godswill Obasohan 25 da Charles Odiase 52 da Okoh Peter 68. An kama su ne a hannun Ekiadolor a cikin al’ummar Ekowe, yayin da bakwai kuma an kama su ne a hanyar Igbe ...
Kimanin mambobin jam’iyyar PDP 18,000 ne a jihar Oyo suka koma jam’iyyar APC.

Kimanin mambobin jam’iyyar PDP 18,000 ne a jihar Oyo suka koma jam’iyyar APC.

Breaking News
Da Duminsa: Mambobin PDP 18,000 sun koma APC a Oyo A karkashin jagorancin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ibarapa ta tsakiya/Ibarapa ta arewa, Muraina Ajibola, masu sauya shekar sun samu tarba daga shugaban jam'iyyar APC Isaac Omodewu, dan takarar Sanatan Oyo ta kudu, Sarafadeen Alli da sauran shugabannin jam'iyyar. A wajen taron akwai mataimakin shugaban jam’iyyar Alhaji Olaide Abas da tsohon sakatare Mojeed Olaoya da sauran shugabannin jam’iyyar a Ibarapaland. Ajibola ya yi alfahari da cewa yana da mabiya kimanin 18,000 da suka zo tare da shi APC, kuma ya roki ‘yan kungiyar da kada su bar jam’iyyar ga masu zuwa su shiga. Omodewu ya ce ya dade yana kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da suka yi korafin kuma korafin ya bada sakamakon mai kyau. Ya kuma yi maraba da wadanda ...
Jam’iyyar APC ta shiga wani hali yayin da sama da mambobinta 5,000 suka sauya sheka zuwa PDP a Katsina

Jam’iyyar APC ta shiga wani hali yayin da sama da mambobinta 5,000 suka sauya sheka zuwa PDP a Katsina

Breaking News
Kimanin mambobin jam’iyyar APC mai mulki a kasa 5,000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a kananan hukumomin Matazu da Musawa na jihar Katsina. Rahotanni sun ce mutanen sun bi shugaban nasu Hon. Ali Maikano, ya koma babbar jam’iyyar adawa saboda musgunawa da shugabannin jam’iyyar APC suka yi musu a lokacin zaben fidda gwanin da ta gudanar a yankin. An tattaro cewa Ali Maikano ya tsaya takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Matazu/Musawa a karkashin jam’iyyar APC amma bai samu nasara ba, don haka ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar saboda abin da ya bayyana a matsayin bijerewa tsarin dimokradiyya wanda ya hana shi samun tikitin tsayawa takara. Da yake karbar wadanda suka sauya sheka a garin Matazu, shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Hon. Salisu Yusuf Majigiri, ya ...
An kama mutane uku da laifin fyade da tilastawa wata yarinya ‘yar shekara 15 shiga kungiyar asiri

An kama mutane uku da laifin fyade da tilastawa wata yarinya ‘yar shekara 15 shiga kungiyar asiri

Laifuka
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar 30 ga watan Yuni ta kama wasu mambobin kungiyar asiri ta Eiye confraternity guda uku, wadanda suka shigar da wata yarinya da karfi cikin kungiyarsu bayan sun yi mata fyade. Wata sanarwa da DSP Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya fitar, ta ce wadanda ake zargin, Daniel Njoku a.k.a Agege, Damilare Ogundiran, da Adebayo Olamilekan, an kama su ne biyo bayan rahoton da mahaifiyar yarinyar ta kai a hedikwatar sashin Ajuwon, wadda ta ruwaito cewa ta aiki ‘yarta ‘yar shekara 15 zuwa wani waje a unguwar Akute Odo, amma Daniel Njoku ya tare mata hanya, inda ya kai ta da karfi wajen ‘yan kungiyarsa a maboyarsu inda aka yi wa yarinyar fyade tare da yi mata dukan tsiya da karfi da kuma tilasta mata shiga Eiye cult group. Mai karar ta...
Hukumar NAFDAC ta rufe gidajen ruwa 10 a Jihar Ondo

Hukumar NAFDAC ta rufe gidajen ruwa 10 a Jihar Ondo

Breaking News
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’ida da ka’idoji. Ko’odinetan hukumar NAFDAC na jihar Ondo, Mista Benu Philip ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Akure. Philip ya ce kamfanonin da abin ya shafa da suka bazu a fadin jihar, akwai wuraren da aka rufe a tsakanin watan Janairu zuwa Yuni. Ya bayyana cewa dukkanin kamfanonin da abin ya shafa suna gudanar da aiki ne da wa’adin lasisin da ya kare da kuma samar da su a cikin yanayi na rashin tsafta. Philip ya ce lasisin da ake basu ba na har abada ba ne, ya kara da cewa ya kamata a ci gaba da sabunta rajistar don guje wa hushin hukumar.
Tinubu zai yi nasara da kashi 60 cikin 100 a zaben 2023 – Okechukwu

Tinubu zai yi nasara da kashi 60 cikin 100 a zaben 2023 – Okechukwu

Siyasa
Darakta-Janar na Muryar Najeriya (VON) kuma mamba a jam’iyyar APC mai mulki, Osita Okechukwu, ya yi hasashen cewa mai rike da tutar jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a babban zaben shekara mai zuwa zai samu nasara da Kashi 60 cikin dari. Ya yi wannan hasashen ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja. Da yake jawabi akan dan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa da za'a yi a watan Fabrairun 2023, Okechukwu ya jaddada cewa jam’iyyar APC za ta lashe zaben da kashi 60 cikin 100 a kan sauran abokan hamayyarsa. Ya kara da cewa; Jihohi 22 na kasar suna karkashin jami'iyyar APC Kuma ko a Majalisar Dokoki ta kasa suke da rinjaye.
Kalli bidiyon yadda wani kwarto ya diro daga gidan sama a lokacin da mijin budurwarsa ya dawo gida

Kalli bidiyon yadda wani kwarto ya diro daga gidan sama a lokacin da mijin budurwarsa ya dawo gida

Auratayya
Wani kwarto ya tsallake rijiya da baya daga hannun mijin wata mata da ya ke lalata da ita a gidan aurenta. Matar auren ta gayyace shi gidan su da ke Lekki a jihar Legas lokacin da mijinta ya fita ya dawo ba tare da ta sani ba, sai ta tilasta wa saurayin tserewa ta hanyar bayan gida. Wani makwabciyarsu ta kama shi a lokacin da yake kokarin dirowa daga benen gidan. Ana iya ganinsa yana tsalle-tsalle daga ginin ya sauka a kasa inda ya dauki tufafinsa ya fara gudu. Makwabciyar ta ce uwar gida ta kan kawo maza gida a duk lokacin da mijinta ba ya nan. Kalli bidiyon a kasa.... https://www.instagram.com/reel/CesxtFeOad-/?igshid=YmMyMTA2M2Y=