fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Author: Abubakar Saddiq

Jam’iyyu 6 ne ake saran zasu fafata a zabukan kanan hukumomi a jihar Borno

Jam’iyyu 6 ne ake saran zasu fafata a zabukan kanan hukumomi a jihar Borno

Siyasa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Borno (BOSIEC) a karkashin Shugabancin shugaban hukumar na jihar Alhaji Abdu Usman ya ce, kimanin jam'iyyu 6 ne a jihar suka amince da shiga zabukan kananan hukumomin jihar wanda hukumar zata gudanar a ranar Asabar. Hakan na kunshe ne ta cikin jawabin da shugaban yayi ga manema labarai a ranar Juma'a a cigaba da shirye-shiryan da hukumar keyi na gudanar da zabukan kananan hukumomin jihar. Ya kuma bayyana jami'iyyun da zasu fafata a zabukan kamar haka: (ADC), Accord Party,  All Progress Congress (APC), All Progressive Grant Alliance (APGA), Peoples Democratic Party (PDP) da kuma Social Democratic Party (SDP).  
COVID-19: An samu karin sabbin mutum 246 A Najeriya

COVID-19: An samu karin sabbin mutum 246 A Najeriya

Kiwon Lafiya
Hukumar dakile ya duwar cututtuka a Najeriya ta fitar da sanarwar samun karin mutum 246 a suka harbu da cutar Coronavirus a Najeriya. A sakon da hukumar ta fitar a daran jiya ya nuna cewa adadin mutum 67,220 ne a ka tabbatar da sun kamu da cutar a fadin kasar. https://twitter.com/NCDCgov/status/1332449685076910082?s=20 Baya ga haka an sallami mutum 62,686 a kasar baki daya.
Gwamnan jihar Kano ya bada umarnin gudanar da gwajin miyagun  kwayoyi  ga ‘yan takarar kananan hukumomin Jihar

Gwamnan jihar Kano ya bada umarnin gudanar da gwajin miyagun kwayoyi ga ‘yan takarar kananan hukumomin Jihar

Kiwon Lafiya
Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci dukkan wadanda suka fito takara a zabukan kananan hukumomi da ke tafe wanda aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Janairun sabuwar shekara, da su tabbata an yi musu gwajin muggan kwayoyi. Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron majalisar zartarwa na jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano. A cewar Mista Garba, Gwamnatin jihar ta yanke shawarar yin hakan ne domin tsabtace jihar Kano daga shan muggan kwayoyi. Ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje na magance shan miyagun kwayoyi tsakanin shugabannin siyasa a fadin jihar.
Hukumar Fasa kauri ta kasa ta cafke kwantenoni 15 na jabun magunguna A jihar Legas

Hukumar Fasa kauri ta kasa ta cafke kwantenoni 15 na jabun magunguna A jihar Legas

Kiwon Lafiya
Mukaddashin kwanturola a sashin aiyukan gwamnatin tarayya, Mista Usman Yahaya ya ce a cikin watanni biyu da suka gabata, rundunar ta cafke kwantena 15 na magungunan jabu da wadanda lokutan amfani dasu ya kare da kuma wasu haramtattun kayayyaki a jihar Legas. Hakanan Kwanturolan hukumar Ya nuna matukar damuwa kan ayyukan wasu bata gari masu shigo da kaya ta tashar jirgin ruwa, da kuma masu fasa-kwaurin wadanda ya ce sun dauki sabbin dabaru kuma a koyaushe suna barazana ga rayukan al'umma sakamakon kin yin abin da ya dace.    
An zargi wasu makiyaya da yin garkuwa da mutane uku tare da neman fansar Naira miliyan N1.2 A Jihar Kogi

An zargi wasu makiyaya da yin garkuwa da mutane uku tare da neman fansar Naira miliyan N1.2 A Jihar Kogi

Crime
Wasu da ake zargin makiyaya ne sun yi garkuwa da wasu ma’aikatan kamfanin karafa na Ajaokuta Steel Company Limited (ASCL) a jihar Kogi. An rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, a kusa da rukunin ma'aikatan kamfanin SAE, yayin da makiyayan suka yi wa wadanda su Kai garkuwa dasu kwantan bauna, dauke da muggan makamai suka kuma tilasta musu shiga daji, kamar yadda wasu mazaunan yankin suka shaida hakan. Wata majiya daga dangin wadanda lamarin ya rutsa dasu sun shaida cewa masu garkuwan sun tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa inda su ka nemi a ba su Naira miliyan 1.2 kudin fansa kafin su sake su. A cewar wasu mazauna yankin sun bayyana cewa, Makiyayan sun kama a kalla mutane 4 amma sun saki mutum daya kasancewar bashi da lafiya kuma tsoho ne mai yawan shekaru. Da aka tun
Hadirin Mota ya lakume rayukan mutane 109 A jihar Ogun daga watan Janairu zuwa Ogusta

Hadirin Mota ya lakume rayukan mutane 109 A jihar Ogun daga watan Janairu zuwa Ogusta

Uncategorized
A ranar Alhamis din da ta gabata ne, hukumar kiyaye haddura reshan jihar Ogun (TRACE), ta sanar da cewa, a kalla mutum 109 ne suka rasa rayukansu a hadurra da suka faru a fadin jihar Ogun tsakanin watan Janairu zuwa watan Agusta. Kwamandan rundunar Mista Seeni Ogunyemi ne ya bayyana hakan a wajen taron kwamandojin rundunar TRACE Corps na shekara-shekara karo na 5, wanda aka gudanar a Valley View, dake Abeokuta. Ya zargi cewa, gudun wuce sa"a da tuki cikin rashin bin doka sune ummul-aba'isin da su ke haifar da yawan hadarurruka akan hanyoyi wanda suke janyo mace-mace a jihar. A cewarsa, a kalla mutane 450 ne suka samu raunuka a hadurru mota daban-daban da su ka afku a tsakanin lokutan. Hakanan kwamandan rundunar ya yabawa gwamnatin jihar bisa gudunmawar da take bawa hukumar na k...
An bukaci Mawadata da su kasance masu tallafawa Mabukata – A cewar Shugaban gidauniyar Zakka (ZSF)

An bukaci Mawadata da su kasance masu tallafawa Mabukata – A cewar Shugaban gidauniyar Zakka (ZSF)

Uncategorized
An yi kira ga MUSULMAI, musamman mawadata daga cikinsu, da su raba abin da suka mallaka ga matalauta da maƙwabta waɗanda basu da hali, domin samun rahama a wajan Allah kasancewar Sadaka wani Nau'ine na ibada kuma aiki ne na masu tsoran Allah. Wannan nasihar ta fito ne daga wani malamin addinin musulinci, Imam Abdulfatah Abdulsalam, a garin Akure, dake jihar Ondo, yayin rabon kayan tallafi, da kuma tsabar kudi ga marassa karfi a karkashin gidauniyar Zakka da Sadaqqah Foundation (ZSF). A cewar Imam Abdulfatah Daurewar zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma na samuwa ne muddin idan Mawadata su ka fidda dokiyoyin su wajan tallafawa mutanan da su ke da bukata. Hakanan Wani bawan Allah da ya amfana da tallafin kudi mai suna Taofiqah Suleiman, ya godewa Allah tare da nuna farin cikin
Gwaman jihar Kano ya rattaba hannu kan kudurin dokar ba da ilmi Kyauta kuma wajubi a Jihar

Gwaman jihar Kano ya rattaba hannu kan kudurin dokar ba da ilmi Kyauta kuma wajubi a Jihar

Uncategorized
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu kan kudurin dokar ba da ilimi kyauta kuma wajubi a jihar. Ganduje ya sanya hannu kan kudirin dokar ne, a gidan gwamnatin jihar a ranar Laraba. Ana sa ran dokar zatai aiki ne akan kowane yaro da ya isa zuwa makaranta, inda aka bukaci iyaye da wajubi su sanya yaran su a makaranta. Hakanan dokar za ta hukunta  dukkan wasu iyayan da su ka ki tura yaran su makaranta.
COVID-19: An samu karin sabbin mutum 169 A Najeriya

COVID-19: An samu karin sabbin mutum 169 A Najeriya

Kiwon Lafiya
Hukumar dakile ya duwar cututtuka a Najeriya ta fitar da sanarwar samun karin mutum 169 a suka harbu da cutar Coronavirus a Najeriya. A sakon da hukumar ta fitar a daran jiya ya nuna cewa adadin mutum 66,74 ne a ka tabbatar da sun kamu da cutar a fadin kasar. https://twitter.com/NCDCgov/status/1332101094403661824?s=20 Baya ga haka an sallami mutum 62,585 a kasar baki daya.
Yadda jami’an rundunar ‘yan sandan jihar kano su ka cafke wani Dilan tabar wiwi a jihar

Yadda jami’an rundunar ‘yan sandan jihar kano su ka cafke wani Dilan tabar wiwi a jihar

Crime
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta cafke wani haramtaccen mai fataucin miyagun kwayoyi, Kabiru Mahmud dan shekara 21 a Danbare dake karamar hukumar Kumbotso, tare da wasu buhhunan busassun ganyan tabar wiwi 49. Daya ke tabbatar da kamun matashin Kakakin rundunar 'yan sandan jihar DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da cafke Mai laifin ga manema labarai a Kano ranar Laraba. Ya bayyana cewa a ranar 24 ga watan Nuwamban shekara 2020, jami'an 'yan sanda na Puff adder yayin da suka kai samame maboyar masu aikata laifi a yankin Danbare, sun kama wanda ake zargin tare da kayayyakin da ake zargin tabar wiwi ne. A lokacin  da rundunar 'yan sandan ke bincikar Matashin ya fallasa cewa, Tabar wiwin mallakar mahaifin sane wanda yakasance Dilanta ne.