fbpx
Friday, January 15
Shadow

Author: Abubakar Saddiq

Cutar Coronavirus ta kashe kimanin mutum dubu 60 a fadin duniya

Cutar Coronavirus ta kashe kimanin mutum dubu 60 a fadin duniya

Kiwon Lafiya
Izuwa yanzu cutar Coronavirus ta halaka mutum dubu 60 a fadin duniya. Rahotan majalisar dinkin duniya A yanzu wanda suka kamu da cutar ya kai mutum miliyan 1 daya da dubu 200. Majalisar dinkin duniya ta bayyana adadain wanda suka kamu da cutar sun fito ne daga kasashen duniya 190. Baya ga hakan an tabbatar da mutum 211,600 da suka warke daga cutar. Cutar Corona ta zamewa duniya rigar kaya wanda hankalin duniya ka cokan ya koma kanta domin dakile ya duwarta a fadin duniya gaba daya.
Labari mai dadi daga jihar yobe sakamakon gwajin wanda ake zargi da ya kamu da cutar Coronavirus bayanai sun nuna bai kamu da cutar ba

Labari mai dadi daga jihar yobe sakamakon gwajin wanda ake zargi da ya kamu da cutar Coronavirus bayanai sun nuna bai kamu da cutar ba

Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar yobe a yau asabar ta tabbatar da wanda ake zargin ya kamu da cutar Coronavirus da cewa ba ya dauke da cutar. Malam idi Gubana matai makin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin kula da cutar Covid-19 a jihar ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Kamar yadda muka rawaito muku a jiya cewa an aike da jini wani mutum mai kimanin shekaru 30 zuwa Abuja domin bincika ko yana dauke da cutar Covid-19 inda kuma ake sa ran sakamakon zai fito nan da cikin awanni 48 masu zuwa wanda, Kwamishinan Lafiya Dr. Mohammed Lawan Gana ne ya bayyana haka. Yanzu dai jihar yobe babu wanda cutar ta kama.
Jimillar kudaden da Najeriya ta samu daga bangarori daban daban domin tallafawa wajan yaki da cutar Covid-19 ya kai naira biliyan N19.488b

Jimillar kudaden da Najeriya ta samu daga bangarori daban daban domin tallafawa wajan yaki da cutar Covid-19 ya kai naira biliyan N19.488b

Kiwon Lafiya
Jummullar kudaden da Najeriya ta samu daga bangarori daban daban domin tallafawa wajan yaki da cutar Covid-19 ya kai naira biliyan N19,488,500,000.00 (N19.488b) Babban bankin kasa tare da attajirin dan kasuwa Aliko dangote sune wanda suka bayar da kudi kimanin biliyan 2 ko wannan su. Sannan sauran wanda suka bayar da kimanin naira biliyan dai dai sune Alhaji Abdulsamad Rabiu Bua, sai Segun Agbaje Guaranty Trust Bank (GTB), sai Tony Elumelu United Bank for Africa (UBA), sai Oba Otudeko First Bank, sai Jim Ovia Zenith Bank , sai Herbert Wigwe Access bank, sai Femi Otedola Amperim Power Distribution limited, sai Raj Gupta African Steel Mills Nigeria Ltd sannan kuma Modupe da Folorunso Alakija Famfa Oil. Sai sauran masu bada gudun mawa sune Pacific Holding Limited wanda y...
COVID-19: Tsohon tauraron Barcelona Xavi Hernandez da matarsa ​​sun ba da gudummawar Euro miliyan ɗaya

COVID-19: Tsohon tauraron Barcelona Xavi Hernandez da matarsa ​​sun ba da gudummawar Euro miliyan ɗaya

Wasanni
Tsohon tauraron Barcelona Xavi Hernandez da matarsa ​​sun ba da gudummawar Euro miliyan ɗaya ($ 1.08 miliyan) zuwa Asibiti na birnin don taimakawa wajan yaki da cutar coronavirus. Xavi Hernandez da matar sa Nuria Cunillera sun bayar da kyautar Euro miliyan ɗaya ga asibitin don taimakawa wajan fuskantar yaki da cutar COVID-19. Daga bisa nine asbitin ya nuna godiyarsa da tallafin da dan wasan da matarsa suka bayar inda asbitin ya aike da sakon godiya ta shafinsu na sada zumunci a ranar asabar.
‘Abin da ya ba ni karfin gwiwar in auri mata biyu a rana guda>>ango Ibrahim Kasimu Oboshi

‘Abin da ya ba ni karfin gwiwar in auri mata biyu a rana guda>>ango Ibrahim Kasimu Oboshi

Auratayya
Wani manomi dan shekaru 35 da haihuwa kuma mai wakiltar mazabar Iwogu a karamar hukumar Keana ta jihar Nasarawa, Ibrahim Kasimu Oboshi, wanda aka fi sani da Ogah, ya auri wasu mata biyu a rana daya. Ya auri Nazira Dahiru Ozegya da Rabi Isyaku Akose a ranar 28 ga Maris, 2020. A lokacin da yake Magana da jaridar Daily Trust a ranar Asabar, ya ce, “Ni maraya ne, mai yin noma kuma a yanzu ni kansila ne. A matsayina na maraya, na ɗauki noma da makaranta da muhimmanci, da harkar noma ne, na sami damar kula da mahaifiyata da kaina. Daga baya ne, na ci zabe don wakiltar garina. ”   Ya ce lokacin da mutane da yawa suka ji yana shirin auran mata biyu, sai suka yi mamaki ko shi ɗan sarki ne ko ɗan wani attajiri ne, amma an gaya musu cewa ni manomi ne. "A gaskiya na rike noma da matu
Ana gudanar da bincike akan  wani mutum da ake zargin ya kamu da cutar Coronavirus a jihar yobe inda ake dakon sakamakon gwajin nashi daga abuja

Ana gudanar da bincike akan wani mutum da ake zargin ya kamu da cutar Coronavirus a jihar yobe inda ake dakon sakamakon gwajin nashi daga abuja

Kiwon Lafiya
Zargin cutar Coronavirus yasa an aike da jini wani mutum mai kimanin shekaru 30 zuwa Abuja domin bincika ko yana dauke da cutar Covid-19 inda kuma ake sa ran sakamakon zai fito nan da cikin awanni 48 masu zuwa, Kwamishinan Lafiya Dr. Mohammed Lawan Gana ne ya bayyana haka. Kwamishinan, wanda ya bayyana lamarin ga manema labarai a maraice Jumma'a, Amma ya ce ba za a iya bayyana mara lafiyan a matsayin wanda ya kamu da cutar COVID 19 ba har sai abun da sakamakon ya nuna daga Abuja. A cewar Kwamishinan, mara lafiyar direban mota ne mai shekara 30, wanda ya zo daga Legas zuwa Potiskum amma bai yi cuɗanya da danginsa ko makwabtan sa ba. Ya ce,: “An gabatar da diraban motar a matsayin mara lafiya a ranar 2 ga Afrilu 2020 tare da alamun tari, zazzabi da wahalar numfashi na kwa
COVID-19: “A shirye muke mu kwashe  yan Najeriya da ke son dawowa daga kasashen waje, in ji gwamnatin tarayya

COVID-19: “A shirye muke mu kwashe yan Najeriya da ke son dawowa daga kasashen waje, in ji gwamnatin tarayya

Siyasa
Gwamnatin tarayya tace a shirye suke su kwashe yan Najeriya da ke son dawowa daga kasashen waje. Gwamnatin wadda ta nuna aniyarta na kwashe ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen waje wadanda ke fatan dawowa gida sakamakon cutar COVID-19. Ministan Harkokin Waje, Mista Geoffrey Onyeama ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a yayin taron tattaunawa na yau da kullun na Kwamitin Shugaban Kasa kan cutar COVID-19 a Abuja. Game da wannan, in ji shi, ma'aikatar tuni ta yi magana da ofisoshin jakadancin Najeriya zuwa kasashen waje don tantance yadda 'yan Najeriya za su bayyana sha'awarsu. Ya kara da cewa ofishin sa tuni ya aike da sakonni ga dukkan ofisoshin jakadanci da kuma ofisoshin da suka dace don tantance 'yan Najeriya da ke son komawa gida saboda COVID19. A cewar sa da zaran an gama
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Sojojin Najeriya da su hada hannu da ‘yan sanda domin dakile ayyukan yan bindiga da ke haifar da hargitsi a wasu sassan kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Sojojin Najeriya da su hada hannu da ‘yan sanda domin dakile ayyukan yan bindiga da ke haifar da hargitsi a wasu sassan kasar

Siyasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarninne ga Sojojin Najeriya da su hada hannu da ‘yan sanda domin dakile‘ ayyukan yan bindiga da ke haifar da hargitsi a wasu sassan kasar. Umurnin Shugaban yazo ne bayan wasu hare hare da suka faru kwanannan a sassan Sakkwato da Filato inda aka ruwaito mutane 22 da kuma mutum 10 sun mutu a jihohin biyu. Umarnin ya fito ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu ya fitar ranar Juma'a. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Sojojin Najeriya da su hada karfi da‘ yan sanda tare da fatattakar ‘yan fashi daga dazuzzukan da ke kasar nan, musamman a wuraren da suka sha fama da hare-hare kwanan nan. Shugaban kasan ya ba da umarnin ne a game da kisan mutane 22 a jihar
Nan bada jimawa ba gungun likitoci daga kasar Chana za su iso Najeriya domin tallafawa kasar wajan yaki da cutar Covid-19

Nan bada jimawa ba gungun likitoci daga kasar Chana za su iso Najeriya domin tallafawa kasar wajan yaki da cutar Covid-19

Kiwon Lafiya
Bayan nasarar da kasar chaina ke samu wajan yaki da cutar Covid-19 ya zuwa yanzu kasar ke ta kokari wajan magance matsalar a fadin duniya baki daya ta hanyar taimakawa wasu kasashe dan dakile ya duwar cuta gaba daya. Da alamu kasar najeriya ita ma tabi sahun samun wannan taimako idan mukai duba da bayanin ministan lafiya, inda Gwamnatin tarayyar ta ce wani gungun Kwararrun likitoci 18 da suka hada da likitoci da ma'aikatan jinya daga kasar Chaina za su isa Najeriya nan da yan kwanaki. Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron tattaunawa na yau da kullum na kwamitin shugaban kasa kan COVID-19 a Abuja ranar Juma’a. Ehanire ya kuma ce, wasu kamfanonin kasar Sin da ke aiki a Najeriya, su ma sun bayar da tallafin su don tai makawa Najeriya a