
Hadarin Mota Ya lakume rayukan mutane 5 A Jihar Legas
Hadarin Mota yayi sanadin salwantar rayukan mutane 5 A kan titin Ibadan zuwa Legas
Wani mummunan hadarin mota da ya afku a kan babban titin Legas zuwa Ibadan ya lakume rayukan mutane 5.
Hadarin wanda ya faru a ranar Laraba, A cewar jami'an hulda da Jama'a na rundunar TRACE Babatunde Akinbiyi ya shaida cewa al'amarin ya rutsa da wata motar Mazda mai lamba LAGOS EPE 575 XA tare da wata Babbar mota mai lamba LAGOS APP 397 YA.
An rawaito cewa, A kalla maza 4 ne hadi da Mace 1 suka rasa ransu a hadarin yayin da wanda suka samu raunuka aka aike dasu Asbiti.