fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Author: Ahmad A

Dakarun soji sunyi nasarar ceto mutane bakwai a hannun ‘yan bindigar jihar Kaduna

Dakarun soji sunyi nasarar ceto mutane bakwai a hannun ‘yan bindigar jihar Kaduna

Tsaro
Dakarun sojin Najeriya sunyi nasarar ceto mutane bakwai a hannun 'yan bindigar karamar hukumar Birnin Gwari da kuma Chikun na jihar Kaduna. Kwamishinan tsaro na jihar ne ya bayyana hakan, Samuel Aruwan inda yace sunyi nasarar ceto su ne bayan sunyi musayar wuta a tsakaninsu. Yace 'yan bindigar sun tsere cikin daji ne domin hukumar taci karfinsu, kuma mutanen da aka ceto sun hada da wata mata da yaranta guda hudu.
Tauraron dan wasan Najeriya, Mikel Obi yayi ritay daga wasan tamola

Tauraron dan wasan Najeriya, Mikel Obi yayi ritay daga wasan tamola

Uncategorized, Wasanni
Tauraron dan wasan Najeriya kuma tsohin kaftin dinta, Mikel Obi ritaya daga wasan Tamola. Dan wasan Najeriya yayi nasarar lashe kofuna a wasan tamola hadda na zakarun nahiyar turai a shekarar 2012 a kungiyar Chelsea dama wasu kofunan. Kuma kafin ritayar tasa ya tala leda ne da kungiyar Kuwait. Obi ya bayyana ritayar tasa ne a shafinsa na Instagram inda mika sakon godiyarsa ga kocawansa da kungiyoyi da abokan aiki dama masoya bakidaya.
Da Dumi Dumi: Yan bindiga sun kashe sojoji da ‘yan sanda marasa adadi a jihar Enugu

Da Dumi Dumi: Yan bindiga sun kashe sojoji da ‘yan sanda marasa adadi a jihar Enugu

Tsaro
Wasu tsageran 'yan bindiga sun kaiwa hakadar jami'ai hari a kudancin jihar Enugu inda suka kashe su gabadayansu suna kan aiki a jiya ranar talata. Wannan lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:30 na safe a daidai a madakatar jami'an dake Obeagu-Amodu, kuma sun kai masu harin ne a motoci. Sun budewa hadakar jami'an wuta har sai da suka kashesu gabadaya basu bar ko daya ba a cewar manema labarai na PUNCH. Kuma kafin su kai masu wannan harin sun sha zuwa madakatar jami'an suna hallakasu da wasu mutanen da basuji basu gani ba, amma wannan karin lamarin yayu kamari sosai.
Sanatoci sunyi watsi da kudurin kafa dokar karba karba da zata baiwa kowace kabila damar shugabanci a Najeriya

Sanatoci sunyi watsi da kudurin kafa dokar karba karba da zata baiwa kowace kabila damar shugabanci a Najeriya

Breaking News, Siyasa
Majalissar dattawa tayi watsi da kudurin kafa dokar karba karba wadda zata baiwa kowace kabila damar mulkar Najeriya. Sanatan dake wakiltar kudancin jihar Benue, Abba Moro ne ya nemi a kafa wannan dokar, amma sai dai burin nasa bai cika ba domin abokan aikin nasa sun juyawa shawarar tashi baya. Inda wasu daga cikinsu suka bayyana cewa kudin tsarin mulki ya baiwa kowa damar tsayawa takarar neman shugabanci saboda haka ba sai an kafa dokar ba. Inda wasu suka bayyana cewa tsohon shugaban kasa GoodLuck Ebele Jonathan yayi mulki ba tare da an kafa wannan dokar ba.
PDP na zolayar APC bayan Buhari ya bukaci a cire Keyamo a matsayin mai magana da yawun kamfe na Tinubu saboda ya soki gwamnatinsa

PDP na zolayar APC bayan Buhari ya bukaci a cire Keyamo a matsayin mai magana da yawun kamfe na Tinubu saboda ya soki gwamnatinsa

Siyasa
PDP na zolayar jam'iyyar adawa ta APC bayan shugaba Buhari ya bukaci a cire Fetus Keyamo a matsayin mai magana da yawun kamfe ne Tinubu saboda yana sukar gwamnatinsa. Mai magana da yawun kungiyar kanfe na Atiku Abubakar, Phrank Shaibu ne ya zolayi jam'iyyar adawar tasu ta APC inda yace jigonsu Fetus Keyamo shima kansa ya san cewa Buhari ya gaza, Saboda haka bai kamata a bar APC ta sake yin shugabanci a Najeriya ba domin Fetus yace al'ummar Najeriya na cikin yunwa, wanda hakan yasa fadar shugaban kasan ta bukaci a cire shi a matsayin mai magana da yawun kamfe na Tinubu.  
‘Yan bindiga sun kashe manoma sunyi garkuwa da mutane 22 a jihar Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe manoma sunyi garkuwa da mutane 22 a jihar Kaduna

Tsaro
Wasu tsageran 'yan bindiga sunyi garkuwa da mutane 22 a jigar Kadhna bayan sun kashe wasu manoma a karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna. Shugaban kungiyar 'yan Birnin Gwarin  ne ya bayyana hakan wato Ishaq Kasai inda yace manoma uku suka kashe a harin da suka kai masu ranar asabar sai kuma sukayi garkuwa da mutane 22. Yace sun kai wannan hare haren ne a yankin Hayin Gada, Damari da kuma Kazage dake karamar hukumar. Amma dai har yanzu hukumar 'yan sanda bata yi tsokaci akan wannan aika aikarda 'yan ta'addan suka aiwatar ba.
Hukumar ‘yan sanda ta kama ‘yan ‘uwa uku a jihar Kebbi bayan sun kashe wanda suke zargi ya sace masu babur

Hukumar ‘yan sanda ta kama ‘yan ‘uwa uku a jihar Kebbi bayan sun kashe wanda suke zargi ya sace masu babur

Laifuka
Hukumar 'yan sandan jihar Kebbi sun damke wasu 'yan uwa guda uku bayan sun kashe wani mutun, Abbas Abubakar wanda suke zarginsa da sace masu babur. Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar ne ya bayyana hakan, Abubakar Nafi'u inda yace sun kama sune bayan sun aikata wannan bannar ta kisan kai. Yace sunje gidan wanda suke zargi ne suka kama shi suka daure shi kana suka lakada masa dan banzan duka kafin suka mika shi hannun hukuma. Wanda bayan kaishi asibiti aka samu labari cewa ya mutu su kuma hukumar ta kama su za a kaisu kotu domib su fuskanci hukunci kan bannar da suka aikata. A karshe hukumat tayi kira ga jama'a su daina daukar hukunci a hannunsu.
‘Yan sandan DSS kwalaben magani biyu suke ba Nnamdi Kanu a madadin bakwai daya kamata su bashi, cewar luyan IPOB

‘Yan sandan DSS kwalaben magani biyu suke ba Nnamdi Kanu a madadin bakwai daya kamata su bashi, cewar luyan IPOB

Uncategorized
Lauyan shugaban haramaracciyar IPOB, Ifeanyi Ejiofor ya bayyana cewa hukumar 'yan sandan DSS dake tsaron shugabansu basa kula da lafiyarsa yadda ya kamata. Inda ya bayyana cewa hatta maganinsa kwalabe bakwai ne ya kamata ace ana bashi amma su kam basu damu ba kwalabe biyu kacal suke bashi, saboda haka ya kamata su bari iyalansa su kula dashi. A karshe yace rashin lafiyar shugaban nasa wanda ya kwashe sama da watanni 14 a kurkuku yayi kamari sosai, saboda haka ya kamata su bari 'yan uwansa au kula da lafiyarsa tunda su ba zasu iya ba.
Kungiyar Yarabawa ta Afenifere tace Obi zata yi ba zata yi Tinubu ba

Kungiyar Yarabawa ta Afenifere tace Obi zata yi ba zata yi Tinubu ba

Siyasa
Kungiyar Yarabawa ta Afniefere ta bayyana cewa ba zata yi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ba, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu a zabe mai zuwa ba. Tinubu ya kasance tsohon gwamnan jihar Legas kuma shi din Bayarabe ne amma duk da haka kungiyar tace bazata yi shi ba domin ita cancanta zatayi ba kalibilanci ba. Shugaban kungiyar Ayo Adebanjo ne ya bayyana hakan a babban birnin tarayya Abuja ranar litinin. Inda yace tsohon gwamnan Anambra zasu zaba wato Peter Obi da jam'iyyar Labour Party domin ba a taba baiwa Inyamurai dama sun mulki Najeriya, saboda haka zasu tsaya masa don yayi nasara.  
Osinbajo yayi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro a taron bikin zagayowar ranar samun ‘yanci karo na 62

Osinbajo yayi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro a taron bikin zagayowar ranar samun ‘yanci karo na 62

Siyasa, Tsaro
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo yasha alwashin kawo karshen matsalar tsaro a taron bikin zagayowar ranar samun 'yanci karo na 62. Najeriya ta samu 'yanci ne a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960 daga hannun turawa. Yayin da mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo yasha alwashin kawo zaman lafiya mai dorewa da kuma cigaba a Najeriya bakidaya. Ya bayyana hakan a wani da suja gudanar ranar lahadi a cocinsu dake babban birnin tarayya Abuja, kuma yace Uban Giji yayi alkawarin kawo zaman lafiya a Najeriya mai dorewa.