
Me gadi ya dirkawa ‘yan mata 3 ciki
Hankula sun tashi a makarantar Queen’s Convent School in Awka Dake jihar Anambra bayan da me gadin makarantar ya dirkawa dalibai 3 ciki.
Duka daliban da yawa cikin suna ajin SS3 ne.
Me gadin dai ya fara aiki ne watanni kadan da suka gabata kuma yana da shekaru sama da 30 kuma ya fito ne daga jihar Akwa-Ibom.
Jaridar Punchng tace zuwa yanzu dai ba'a san matakin da makarantar zata dauka akan me gadin ba.
Wata malama a makarantar ta bayyana cewa basa goyon bayan daukar matashi a matsayin me gadi amma hukumar makarantar taki yadda.
Gashinan yanzu abinda ba'a so ya faru.
Wasu iyaye dai sun yi barazanar cire 'ya'yansu daga makarantar.