Sunday, June 7
Shadow

Author: hutudole

Gwamna Ganduje Ya Rabawa Fulani Makiyaya Gidaje Kyauta

Gwamna Ganduje Ya Rabawa Fulani Makiyaya Gidaje Kyauta

Uncategorized
Mai Girma Gwamna, Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya jagoranci kaddamar da rabon gidaje kyauta domin inganta harkokin kiwo da rayuwar fulani makiyaya a fadin Jihar Kano wanda aka gabatar a dajin Dansoshiya dake karamar hukumar Kiru karkashin kwamitin duba wajen tabbatar da RUGA da kasuwar Nono karkashin Dr Jibrilla Muhammad.     Gwamna Ganduje ya ce kasancewar sa Bafulatani Makiyayi kafin kasancewar sa Gwamnan, ya zama lallai ya tallafawa makiyayan wanda hakan zai inganta rayuwar su data yayansu.   A yau an fara rabon gidaje 25 da aka kammala daga cikin gidaje 200 wanda Gwamnatin zata gina a wannan daji Sannan anyi rijiyoyin butsatse don shan ruwan shanunsu a gurare 5 cikin dajin tare da aikin gina dam wanda aikinsa ya tsaya saboda damina.   C...
Gwamna El-Rufa’i ya amsa cewa akwai yiyuwar ana bayyana sakamakon karya na Coronavirus/COVID-19

Gwamna El-Rufa’i ya amsa cewa akwai yiyuwar ana bayyana sakamakon karya na Coronavirus/COVID-19

Uncategorized
Gwamnan jihar Kaduna,Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya amsa cewa akwai yiyuwar matsala a sakamakon da ake samu na cutar Coronavirus/COVID-19.   Ya amsa hakanne bayan da wani yayi korafin cewa akwai yiyuwar wasu gwamnonin da gangan sun fara kin mika adadin yawan samfurin jinin da ake bukata dan kada su samu masu cutar Coronavirus/COVID-19 da yawa. Gwamna El-Rufa'i yace wannan magana ka iya zama gaskiya amma dai a sani Kaduna, Abuja da Legas basa cikin masu yin wannan abu. Inda yace suna bibiyar duk wata matsalar cutar Coronavirus/COVID-19 dan su gano a kuma musu gwajin wanda aka samu da ita dan basa so a samu "Macemacen da zasu kaya bayanin yanda aka samesu"   https://twitter.com/elrufai/status/1269226040976707589?s=19 A baya dai an samu mace-mace a Musamman Kan...
Kisan ‘yansanda a Jihar Kogi:Makaman da aka baiwa Matasane a zaben daya gabata da ba’a kwace ba ya jawo wannan matsalar>>Dino Melaye

Kisan ‘yansanda a Jihar Kogi:Makaman da aka baiwa Matasane a zaben daya gabata da ba’a kwace ba ya jawo wannan matsalar>>Dino Melaye

Siyasa
Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa fashin da aka yi a jihar Kogi wanda yayi sanadin mutuwar 'yansanda makaman da aka baiwa matasane a lokacin zaben da ya gabata da ba'a kwace ba ya jawoshi.   Sanata Melaye ya bayyana haka ta shaginshi na sada zumunta. A makon da ya gabata ne dai wasu 'yan fashi suka shiga garin Isanlu dake jhar Kogin suka kashe jami'an 'yansanda tare da yin fashi a wani banki.
Watakila Jadon Sancho yayi irin yarjejeniyar Cristiano Ronaldo wadda zata sa shi ya koma Manchester United

Watakila Jadon Sancho yayi irin yarjejeniyar Cristiano Ronaldo wadda zata sa shi ya koma Manchester United

Uncategorized
Borussia Dortmund sun yarda cewa Sancho zai bar kungiyar su a wannan kakar wasan saboda Manchester United sun nemi shi a shekarar data gabata, a cewar gwanin Bundlesliga kuma tsohon dan wasan Norway Jan Age Fjortoft. Jadon Sancho shine babban dan wasan da Man United zasu siya idan aka bude kasuwar yan wasa, yayin da dan wasan Ingilan yayi nasarar jefa kwallaye guda 17 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye guda 16 a wannan kakar wasan. Fjortoft ya tabbatar da cewa Dortmund sun san Sancho yana so ya bar su a wannan shekarar. Mai sharhin wasannin ya gayawa ESPN FC cewa, a koda yaushe Dortmund suna fatan adana yan wasan su amma daga karshe kuma su rasa su. Shi yana jin cewa a kakar wasan bara Dortmund sunyi irin yarjejeniyar da Ronaldo yayi da United yayin da Sir Alex Ferguson yace mai ...
Madrid sun shirya fasa siyan gabadaya yan wasan da suke hari domin su samu damar siyan Mbappe a kakar wasa mai zuwa

Madrid sun shirya fasa siyan gabadaya yan wasan da suke hari domin su samu damar siyan Mbappe a kakar wasa mai zuwa

Wasanni
Kungiyar zakarun La Liga Real Madrid da Liverpool suna harin siyan tauraron dan wasan faransa Kylian Mbappe mai shekaru 21 daga kungiyar PSG wanda ya lashe gasar kofin duniya a shekara ta 2018. Manema labarai na kasar faransa Le10 Sport sun sanar cewa kungiyar Madrid sun shirya fasa siyan gabadaya yan wasan da suke hari domin su mayar da mayar da hankalin su gabadaya wajen siyan Kylian Mbappe a kakar wasan badi. Ana sa ran cewa farashin dan wasan faransan zai kafa sabon tarihi a kasuwar yan wasan kwallon kafa, kuma Real Madrid sun shirya fasa siyan Sancho domin su ba kansu damar siyan Mbappe a kakar wasa mai zuwa. Duk da haka dai ko Madrid sun nemi su siya Mbappe a kakar wasa mai zuwa, An bukaci dan wasan mai shekaru 21 cewa ya koma Liverpool saboda zai zamo sarki a gasar Pr...
Kayataccen hoton Gwamna El-Rufai da iyalansa: Ji maganar da matar Gwamnan da wani suka yi kan Matsalar Rayuwa

Kayataccen hoton Gwamna El-Rufai da iyalansa: Ji maganar da matar Gwamnan da wani suka yi kan Matsalar Rayuwa

Siyasa
Gwamnan Kaduna,Malam Nasir El-Rufai kenan a wannan hoton tare da iyalinsa, matarsa Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ce ta saka hoton a shafinta na Twitter.   Ta mai taken "Baban Munir da maman Amina" inda a karshe tawa mabiyanta fatan Alheri da cewa ina fatan Kuna jin dadin wannan Rana. https://twitter.com/hadizel/status/1269251651367571456?s=19 Saidai wani yace mata Eh amma ba kamar taku ba.   Hajiya Hadiza ta tambayeshi ya tabbata kuwa? Kowa fa nada tashi matsalar. https://twitter.com/hadizel/status/1269254925860601858?s=19   Saidai yace ya tabbata da hakan, dan idan da zasu fada mata matsalolinsu abin dai ba magana... https://twitter.com/hadizel/status/1269258569519714308?s=19 A karshe dai tayi tayi fatan Allah ya kawo saukin Lamarin. Ind...
Taraba: An kashe Limami, Me gari da wasu 3 a sabon hari

Taraba: An kashe Limami, Me gari da wasu 3 a sabon hari

Tsaro
Rikici tsakanun Jukun da Tibi a jihar Taraba yyi sanadin kisan karin mutane 5 a wani tari da aka kai cikin dare, kamar yanda hutudole ya samo.   An kai harinne a kauyen Bagoni inda ama kashe me garin da kuma limamin garin kamar yanda Dailytrust ta ruwaito. Hakanan an kashe wasu karin mutane 3 a Kauyen Wurbo dake karamar hukumar Bali. A jiyane dai muka kawo muku rahoton yanda aka kashe mutane da dama a kauyen Tunga dake wannan karamar hukuma wanda rahotanni suka nuna cewa 'yan kabilar Jibawane dake da alaka da kabilar jukunne suka kaishi.   An kona gidaje da satar kaya na miliyoyin Naira.  Rahoton yace yanzu matasa na kokarin kai harin Ramuwar gayya kan kabilar Tibi wanda yasa 'yan kabikar suka fara tserewa daga gidajensu.   Wannan hare-hare sun kawo
Babu tsari a gwamnatin Buhari, ya kasa shawo kan matsalar tsaro>>PDP

Babu tsari a gwamnatin Buhari, ya kasa shawo kan matsalar tsaro>>PDP

Tsaro
Jam'iyyar Adawa ta PDP ta caccaki gwamnatin shugaban kasa,Muhammadu Buhari kan matsalar tsaron da ke ci gaba da lakume rayuka amma har yanzu aka kasa shawo kanta.   A baya dai munji yanda aka kashe mutane 9 a wani kauye na karamar hukumar Kajuru dake Kaduna. Hakanan a makon daya gabata ne muka ji yanda mutane 23 suka rasa rayukansu a jihar Kogi sanadin wani fasgi da akayi.   Da PDP take magana akan wadanan lamurra ta bayyana cewa rashin daukar mataki akan irin wadannan abubuwa da suka faru ya nuna cewa shugaba Buhari baya iya sarrafa gwamnatinsa yanda ya kamata.   PDP ta bayyana hakane ta bakin sakataren watsa labaranta, Kola Ologbondiya inda tace sun yi tsammanin shugaba Buhari a matsayinshi na tsohon soja zai iya magance matsalar tsaro amma ga dukk...
Babu Wani Talikin Da Za Mu Yi Wa Biyayya Matukar Umarninsa Ta Sabawa Allah Da ManzonSa, Cewar Sheikh Sani Jingir

Babu Wani Talikin Da Za Mu Yi Wa Biyayya Matukar Umarninsa Ta Sabawa Allah Da ManzonSa, Cewar Sheikh Sani Jingir

Uncategorized
Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izalahñ Sheikh Sani Yahya Jingir ya ce "addinin musulunci ya fi raina, ya fi uwata, ya fi ubana, ya fi gwamnoni, ya fi fadar shugaban kasa, ya fi majalisar dinkin duniya.     Don duk abinda za su yi na barazana ba za su iya maka komai ba sai Allah Ya ga dama. Wani irin kaidi ne Fir'auna bai yi wa Annabi Musa ba? Amma Allah Ya kare shi."   Sheikh ya ci gabada cewa ba wani taliki da za mu yi wa biyayyya akan umarnin da ya sabawa Allah da Manzonsa.     Sheikh Jingir ya yi wannan jawaban ne a yayin da yake gabatar da nasihar Juma'a a masallacin Juma'a na 'Yan Taya dake birnin Jos.   A karshe Malamin ya gudanar da addu'ar Allah ya kare musulunci da musulmi daga sharrin masharranta.
Maganar da PSG suka yi tasa Barcelona ba za su iya siyan Neymar ba

Maganar da PSG suka yi tasa Barcelona ba za su iya siyan Neymar ba

Wasanni
Barcelona har yanzu suna da burin dawo da tsohon dan wasan su daya koma Paris saint German a shekara ta 2017 a farashin da ba'a taba siyan wani dan wasan kwallon kafa ba, Amma sai dai maganar da PSG su kayi yanzu tasa Barcelona ba za su iya siyan dan wasan ba. Barcelona suna kokarin yin musaya da wasu yan wasan su wurin siyan Neymar saboda basu da kudin siyan shi a yanzu yayin da suka ba PSG zabin yan wasan su kamar haka, Antoine Griezmann, Samuel Umtiti da Ousmane Dembele da dai sauran su. A koda yaushe PSG suna kokarin siyan yan wasan faransa domin so dawo dasu kasar su, Amma a wannan karin basu yi hakan ba yayin da suka yi burus da gabadaya yan wasan da Barcelona ta basu duk da cewa dukkan su yan faransa ne. Kuma su kansu PSG sun san cewa Neymar yana so ya koma Barcelona. ...