Saturday, June 6
Shadow

Author: hutudole

Makarantar dake bukatar tallafi

Makarantar dake bukatar tallafi

Uncategorized
Kamar dai a wasu makarantun gwamnati na Najeriya wannan wata makarantace a garin Mosul dake kasar Iraki da majalisar dinkin Duniya tace babu isassun litattafai babu isasshen ruwan sha, sannan makarantar bata samun wutar lantaraki yanda ya kamata, amma hakan bai hana yaran makarantar jajircewa ba wajen ganin sun samu abinda ake bukataba, muna fatan wannan makaranta dama namu na Najeriya zasu samu abubuwan da ake bukata dan samun ingantaccen ilimi.
Maza sun fara gane muhimmancin tallafawa mata da ayyukan gida?

Maza sun fara gane muhimmancin tallafawa mata da ayyukan gida?

Uncategorized
Allah sarki wasu mazan nada tausayi, sun fahimci irin yanda mata ke dawainiya da gida da kuma rainon 'ya 'ya shiyasa wani lokutan suke tallafa musu da rainon yara, wani namijin baidama lokacin dazai zauna yayi hira da iyalinshi, shidai neman kudi kawai ko kuma zama a majalisa, wanin kuma ganiyake idan yayi irin wannan to wai za'a rainashine, wallahi ko daya a duk lokacin da kake nunawa abokin zamanka tausayi da tallafamai wajen yin ayyukan da musamman ba muhallinka bane to tabbas akwai wata kima da daraja da kake karawa kanka a gurin wannan mutumin. Sannan kuma yana daya daga cikin abinda zai karama shakuwa da soyayya dasu kansu 'ya 'yan naka, yanzu misali, bayan shekaru da dama bayan danka ko 'yarka ta girma, sai taga irin wadannan hotunan, yanda kake goyata tana yarinya sannan 'ya '...
Wannan hoton ya jawo cece-kuce

Wannan hoton ya jawo cece-kuce

Uncategorized
Kafar watsa labarai ta bbchausa ta saka wannan hoton na shugaban kasa, Muhammadu Buhari da matarshi a kusa dashi sannan da wata baiwar Allah acan ta dayan bangarenshi a shafinsu na sada zumunta da muhawara, sannan sukayi tambayar"Menene sunan wadda take tsaye kusa da shugaba Buhari banda mai dakinshi A'isha?". Wannan tambaya da bbchausa sukayi ta jawo zazzafar muhawara tsakanin mutane, Shin wai kodan waccan din wadda ba A'ishaba tafi matsuwa kusa da Buharine a hoton ko kuwa dan saboda hoton mata da mijine, amma sai gashi wata tazo wadda mutane basu saba ganinta a tare dashi sun sakashi tsakiya?. Gadai hotunan wasu daga cikin ra'ayoyin da mutane suka bayyana akan wannn hoton.
Akwai bukatar a taimakawa wannan yaron yacigaba da karatu saboda hazakar daya nuna

Akwai bukatar a taimakawa wannan yaron yacigaba da karatu saboda hazakar daya nuna

Uncategorized
Shitu Abdullahi Dan Asalin Karamar Hukumar Mallammadori A Jihar Jigawa, Shine Ya fi Kowanne Dalibi Cin Jarabawar WAEC Da JAMB A Jihar Jigawa. Shitu Ya Kamamala Makarantar 'Gifted and Talented' Bamaina A Wannan Shekarar Ta 2017. Inda Ya Samu Distention A Dukkan Darusa 9 Na Jarabawar WAEC, Sannan Ya Sami Maki 306 A Jarabawar JAMB. Sai Dai Babban Abun Bakin Ciki Iyayen Dalibin Ba su Da Halin Da Za su Iya Tura Dan Nasu Jami'a. Akwai Bukatar Gwamnati Ko Masu Hannu Da Shuni Dasu Rinka Taimakawa Hazikan Yara Kamar Shitu Abdullahi, Domin Al'umma Su Amfana Da Ilimi Da Allah Ya Ba su. rariya.