Yan sanda sun ceto wani tsoho mai shekaru 80 da aka sace a Kano
Yan sanda a jihar Kano sun ceto wani dattijo mai shekaru 80, Alhaji Nadabo, da aka yi garkuwa da shi a kauyen Chiromawa da ke karamar hukumar Garun Mallam.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ya ce an kubutar da shi ne biyo bayan rahoton da aka samu a ranar 12/11/2021 da misalin karfe 1957 na safiyar cewa an yi garkuwa da Alhaji Nadabo.
“Da samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya tada tare da umurci rundunar ‘Operation Puff Adder’ da su kubutar da wadanda abin ya shafa tare da kama masu laifin.”
Kiyawa ya bayyana cewa, tare da hadin guiwar ‘yan banga na yankin da sauran al’ummar yankin, an gano masu garkuwa da mutane tare da tilasta musu saki...