
Yan sanda sun kama wasu mutane takwas masu garkuwa da mutane, inda suka ceto mutane hudu a Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane takwas da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da ceto wasu mutane hudu da ta rutsa da su a ayyukan da ta gudanar cikin wata guda a fadin jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya rabawa manema labarai.
Ya ce an kama su ne bisa sahihan bayanan da aka samu cewa, wasu mashahuran ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane na addabar karamar hukumar Tudun Wada, karamar hukumar Doguwa da ke dajin Falgore da wasu sassan jihohin makwabta.
Kiyawa ya ce da yake karbar rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya daga tare da umurci rundunar ‘Operation Puff Adder’ da su kamo wadanda suka aikata laifin.
Ya yi bayanin cewa rund...