
Za a fara gwajin riga-kafin cutar HIV a Afirka ta Kudu
Za a fara gwajin riga-kafin cutar HIV a Afirka ta Kudu
Ƙasashen Afirka ta Kudu da Amurka za su fara gwajin riga-kafin cutar HIV, inda suka yi kira ga mutane da su bayar da haɗin kai domin gudanar da gwajin.
Cibiyar bincike ta Amurka (NIH) ta ce an ƙirƙiri sabon riga-kafin mai suna VIR-1388, domin taimaka wa ƙwayoyin jini masu taimaka wa garkuwar jiki da ake kira 'T-cells', waɗanda ke yaƙar sauran ƙwayoyin cutuka da ke kawo wa jiki hari.
Riga-kafin zai taimaka wajen sanya garkuwar jiki ya samar da ƙwayoyin 'T-cells', waɗanda za su iya gano ƙwayar cutar HIV domin sanar da garkuwar jiki, don ya ɗauki matakin kare jiki daga mummunar illar da ƙwayar za ta yi wa jiki.
Cibiyar bincike ta Amurka NIH, da gidauniyar 'Bill and Melinda Gates' da wani...