
Ma’aikatan wutar lantarki zasu tafi yajin aiki saboda cire tallafin mai
Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki (NUEE) ta baiwa membobinta umarnin dakatar da aiki a fadin Najariya dan fara yajin aiki.
Sakataren Kungiyar, Dominic Igwebike ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fitar.
Yace ma'aikatansu su fara yajin aiki tare da kungiyar kwadago ranar Laraba.