fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Author: wakiliya F.

An hana ajiye gumaka masu tsiraici na tallata kaya a ƙofar shaguna a Tanzania

An hana ajiye gumaka masu tsiraici na tallata kaya a ƙofar shaguna a Tanzania

Uncategorized
An hana ajiye gumaka masu tsiraici na tallata kaya a ƙofar shaguna a Tanzania   Hukuma ta ce ta yi hakan ne domin kare yara da matasa daga gurɓataImage caption: Hukuma ta ce ta yi hakan ne domin kare yara da matasa daga gurɓata Hukumomi a wani lardin ƙasar Tanzaniya sun hana 'yan kasuwa ko teloli ajiye irin gunkin nan na tallata tufafi da sauran kayan sanya wa, wanda ba a rufe jikinsa ba sosai, inda za a iya ganin wani sashe na jiki kamar nono, a ƙofar shagunansu.   Shugaban al'ummar garin Unguja a yankin tsibirin Zanzibar, Rashid Msaraka, ya ce an ɓullo da dokar ne domin kare al'adu da kimar ƙasar.   A wata hira da ya yi da wata kafar yaɗa labarai ta intanet a ƙasar ta gabashin Afirka Mr Msaraka ya ce masu irin waɗannan kasuwanci da ke buƙatar tallata k...
Ana buƙatar sama da dala biliyan ɗaya don taimaka wa arewa maso gabashin Najeriya – MDD

Ana buƙatar sama da dala biliyan ɗaya don taimaka wa arewa maso gabashin Najeriya – MDD

Uncategorized
  Ana buƙatar sama da dala biliyan ɗaya don taimaka wa arewa maso gabashin Najeriya - MDD   Hukumar tsara ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya (OCHA) ta buƙaci dala biliyan 1.3 domin tallafa wa mutane miliyan shida da ke fama da matsaloli da rikicin Boko Haram ya haddasa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.   Wannan na cikin shirin ayyukan hukumar ne da babban jami'inta a Najeriya Mista Matthias Schmale, ya gabatar jiya Alhamis.   Yawan mutanen da ke cikin buƙatar ya ƙaru da 500,000 daga miliyan biyar da 500 da aka tantance a shekara ta 2022, waɗanda yakin na tsawon shekara 13 ya shafa.   Ya ƙara da cewa akwai aƙalla mutum miliyan 2.4 da ke cikin matsanancin halin buƙata, sakamakon riki da bala'o'i da cutuka.   Hukumar ...
Sama da shekaru 50, Marigayi Sa’adu Zungur yayi wannan wa’azin a sigar Wake YACHE:

Sama da shekaru 50, Marigayi Sa’adu Zungur yayi wannan wa’azin a sigar Wake YACHE:

Uncategorized
Sama da shekaru 50, Marigayi Sa'adu Zungur yayi wannan wa'azin a sigar Wake YACHE:   ~ Babu shakka yan kudu zasu hau, ~ Dokin mulkin Nijeriya. ~ In ko yan kudu sunka hau, ~ Babu sauran dadi, dada kowa zai sha wuya. ~ A Arewa zumunta ta mutu, ~ Sai karya sai sharholiya. ~ Camfe-camfe da tsibbace tsibbacen, ~ Malaman karya yan damfara. ~ Sai karya sai kwambon tsiya, ~ Sai sa hula mai annakiya. ~ Ga gorin asali da na dukiya, ~ Sai kace dan annabi fariya. ~ Jahilci ya ci lakar mu duk, ~ Ya sa mana sarka har wuya. Ya sa mana ankwa hannuwa, ~ Ya daure kafarmu da tsarkiya. ~ Bakunan mu ya sa takunkumi, ~ Ba zalaka sai sharholiya. ~ Wagga al’umma mai zata yo, ~ A cikin zarafofin duniya. Kai Bahaushe ba shi da zuciya , ...