Yan uwan mutanen da yan bindiga sukyi garkuwa dasu bayan sun kai hari jirgin kasa a jihar Kaduna sun baiwa gwamnatin tarayya awanni 72 ta ceto masu yan uwansu.
Inda suka bayyan cewa har yanzu kungiyar jiragen kasa ta Najeriya batayi wani yunkurin ceto masu yan uwansu ba, kuma har yanzu yan ta’addan basu kirasu a waya ba domin sasanci.
Sun bayyana hakan ne a wani taro da suka gudanar ranar litinin a jihar Kaduna, inda a karshe sukace idan gwambati ta kasa cetosu cikin wa’adin da suka bata to su zasu ceto yan uwansu.