fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Ayau za’a tsayar da magana akan auren diyar gwamnan Kano, Fatima Abdullahi Ganduje da masoyinta dan gwamnan jihar Oyo, Idris Abiola Ajimobi

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amshi bakuncin kusan gwamnoni goma sha daya ayau Juma’a inda yau din za’ayi gaisuwar iyaye da kuma tsayar da magana akan diyar gwamnan Fatima Abdullahi Ganduje da masoyinta dan gwamnan jihar Oyo Idris Aboila Ajimobi.

Dama dai tun kwanaki ake da rade-radin cewa diyar gwamnan ta nace zata auri bayerabe.

To ayau gashi ya tabbata, amma wannan ba wani abin surutu ko mamaki bane dan duk Allah ya haliccemu kuma ba haramun bane yin hakan a addini. Allah ya tabbatar musu da Alherinsa.

Gwamnonin da suka shiga Kano ayau dan sheda wannan gagarumin abin tarihi sun hada da gwamnan legas, gwamnan katsina, gwamnan Borno, gwamnan Kwara, gwamnan jigawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.