Ayyana Gawuna matsayin Gwamna ya sa na cire kai na daga sahun ‘yan Nijeriya – Adam
“Matashi Adam Longbest yace Insha Allahu Gawuna baze taɓa mulkarsa ba saboda baya buƙatar ƙara ganin azzalumar gwamnati irin wacce ya gani ta Ganduje yasan babu abinda zai sauya tsakanin Gawuna da Ganduje duk irin mulkin ɗaya ne.
“Matashin ya ƙara da cewa maganarma ace Gawuna shine yafi ba ta taso ba tunda Allah ba ya goyon bayan zalîncî, kuma kowa yasan zalîncî akayi wajen ayyanasa da kotu ta ce shine ya yi Nasara ta ina? dan haka shidai baiga wanda zai gamsar dashi akan cewa wannan ba azzâlúmâr gwamnati take mulki tun daga sama wannan shiryaiyan abune.
Bugu da ƙari matashi Adam ya ƙara da cewa ba zai taɓa yiwa Azzalumai biyayya ba kan duk mummunar halayayar su, kuma indai aka ce Gawuna shi ya ƙara yin Nasara a kotu na gaba ta ɗaukaka ƙara tabbas zai bar Nijeriya ba kuma zai dawo ba har se ya kammala wa’adinsa koma yayi zamansa acan saboda gaba ɗaya Nijeriyan haushi ta ke bashi.
“A ƙarshe matashin Ɗan kasuwa Adam Longbest ya ƙarƙare da cewa tabbas ana yiwa Demokradiyya Fyáɗé a Nijeriya, saboda ga abinda talakawa suka zaɓa kuma ga abinda su mahukunta ke so su yi masu ƙarfaƙarfa akan haka, tabbas wannan zaluncine ƙarara ko shakka babu.”