fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

“Ba ayi garkuwa dani ba ni na shiga daji da kaina”>>Mata ta bayar da hakuri bayan ta tayar da hankulan al’umma

A makon daya gabata wata mata mai suna Amira Sufyan ta tayar da hankulan al’umma a kafar sada zumunta ta Twitter cewa anyi garkuwa da ita a baban birnin tarayya Abuja.

Inda tace mutanen da sukayi garkuwa da ita sanye suke da kayan hukumar ‘yan sanda kuma su 17 sukayi gakuwa dasu a wurare daban daban a babban birnin tatayyar.

Amma yanzu ta bayar hakuri cewa wannan labarin karya ne ita ta shiga daji da kanta kuma bayan hukumar su ganta, kuma tace tana bukatar addu’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published.