Maganar fitar da dan takarar shugaban kasa wanda ‘yan Arewa zasu bi a jam’iyyar PDP da aka ce dattawan Arewa sun yi ya dauki sabon salo, saboda kungiyar ta bayyana cewa ba da ita aka yi ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, dattawan Arewa sun zabi Tsohon kakakin majalisar dattijai da kuma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad a matsayin wadanda zasu wakilci Arewa a takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.
Saidai gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya ki amincewa da wannan mataki, inda hakanan shima tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yace baya tare da wannan zaben fidda gwani da aka yi.
Saidai wani sabon rahoto da ake samu daga kungiyar dattawan Arewan ta hannun sakataren yada labaran kungiyar, Dr. Hakeem Baba Ahmad ya bayyana cewa, kungiyar bata siyasa bace kuma basu tare da wancan mataki na fidda dan takara da aka yi.