Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ba dan shi ba da shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai lashe zaben shekarar 2015 ba.
Bola Tinubu ya bayyana hakane a Abeokuta inda yace kuma shine yace a baiwa Yemi Osinbajo takarar mataimakin shugaban kasa.
Yace da shine Shugaba Buhari ya dauka ya zama mataimakinsa amma sai aka ce ba zai yiyu ba saboda kasancewarsu duka musulmai, shine aka mika Yemi Osinbajo.
Tinubu yace bai taba fadar haka ba idan ba yau ba.