fbpx
Monday, March 1
Shadow

Ba duk yan bindinga bane yan ta’adda – Gwamnan Zamfara

 

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce ba duk ‘yan bindigar da ke addabar sassan jihar da sauran jihohin makwabta ba ne masu aikata laifi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya bayyana cewa yawancin ‘yan bindingar suna daukar makami ne saboda rashin adalcin da wasu daga cikin al’umma ke musu.

Yan ta’addan sun kashe da kuma sace daruruwan mutane a jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto, Niger, Kaduna da Nasarawa a shekarun baya.

Sabanin ikirarin da gwamnan ya yi, akwai rade-radin cewa aikata laifuffukan nada nasaba da hako zinari da sauran albarkatun karkashin kasa a wadannan yankuna.

Duk da hare-hare kan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, Mista Matawalle ya sha yin kira ga gwamnatin tarayya da ta yi afuwa ga tubabbun’ yan bindingar.

Yayin da yake bayanin dalilan hare-haren, Matawalle ya ce wadanda aka dora wa alhakin kare lafiyar al’umma wani lokacin sukan saci shanunsu tare da lalata abincinsu.

Ya ce tunda ba su da wanda za su tsaya masu dole ne su kare kansu.

A karshe yace ba dukkan yan bindinga ne a yan ta’adda ba, Idan kayi binciki abin da ke faruwa, da abin da ya sanya su daukar doka a hannunsu shine, wani lokacin wasu da ake kira kungiyar ‘yan banga ne ana hada baki da su ana zaluntarsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *