Kungiyar kare muradub inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta bayyana cewa, ba duka Inyamurai bane ke son kafa kasar Biafra ba.
Tace mafi yawanci basu son a kafa Biafra. Kungiyar ta bayyana hakane tare da jan hankali kan ‘yan Najeriya su goyi bayan Inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023.
Shugaban kungiyar, George Obiozor ya bayyana cewa, shugaban kasa, Inyamuri zai tabbatar da an wa kowa a kasarnan Adalci.
Kungiyar tace bai kamata a mayar dasu saniyar ware ba da nuna cewa basu san zaman lafiya, tace ana yin hakanne dan cimma wata manufa ta siyasa kawai.