Friday, May 29
Shadow

Ba gaskiya bane cewa Taron da ake a Kasuwa yafi na Masallaci>>Gwamna El-Rufai

A hirar da aka yi da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kan dokar zaman gida da ake a jihar.

 

Ya amsa tambayar cewa mutane na korafi an bude kasuwa ana taro me yawa amma ba’a bude masallaci ba.

 

Gwamnan yace ba gaskiya bane wannan magana, yace ya je da kansa kasuwar wucin gadi ya gani yanda masu sayar da kayayyakin suke warawara inda har suka masa korafin cewa akwai rana kuma yasa a samo Tamfal dan saukaka musu.

 

Gwamnan yace shi abinci dolene a Nemeshi amma a Ko ina mutum zai iya yin sallah.

 

Yace sun zauna da malamai kuma sun tabbatar masa da cewa kare rai yafi yin jam’i inda suka gaya masa cewa yayi abinda yake ganin zai fisshe da jama’ar Kaduna.

 

Gwamnan yace akwai masu zagi da suka wanda yace ‘yan PDP ne wanda kuma an kadasu zabe amma har yanzu basu hakura na suna so su zuga jama’a.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *