Tsohon shugaban sojojin Najariya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, ba gidansa ne aka kulle a Abuja ba.
Hukumar ICPC dake yaki da rashawa da cin hanci ta kama wani da motoci da kudi wanda rahotannin farko suka ce na Buratai ne.
Saidai lauyansa, Ugochukwu Osuagwu yace wannan magana ba gaskiya bace. Yace karyace kawai aka hadawa Buratai din.