Fitaccen Daraktan fina-finan Hausa Umar UK ya ce, ba a taba Gwamnan da ya taimaki Kannywood kamar Kwankwaso ba.
UK ya ce, babu dalilin da wani dan Kannywood zai ki goyon bayan tafiyar tsohon Gwamna.
A cewarsa Kwankwaso ya yiwa Kannywood riga da wando ta hanyar mayar da su makaranta a zamanin mulkinsa.
Ga dai bayaninsa.