Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya mayar da martani ga sanarwar da gwamna Hope Uzodimma ya yi na sauya sunan jami’ar Eastern Palm University zuwa K. O. Mbadiwe University wannan ya biyo bayan jim da dan wani marigayi dan siyasa kuma jakada, Greg Mbadiwe ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Sanatan da ke wakiltar Imo ta Yamma wanda ya bayyana cewa an kafa jami’ar ne bisa hadin gwiwar gwamnati da ‘yan kasuwa tsakanin jihar da gidauniyar Rochas, ya kara da cewa zai zama rainin hankali ga Gwamna Hope Uzodimma ya sauya sunan Jami’ar ta Palm.
Okorocha ya kuma yi tir da yadda majalisar dokokin jihar ta soke dokar da ta kafa jami’ar.