Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwasonya bayyana cewa ba karamar dama ya baiwa Peter Obi na amince ya zama abokin takararsa.
Inda yace shi ba zai zama mataimakin Obi ba amma idan har Obi bai amince ba tofa kudu masu gabashin Najeriya zasu tafka babbar asara a wannan zaben mai zuwa.
Kwankwason ya bayyana hakan ne a ranar asabar bayan ya kaddamar da babban ofishin NNPP a jihar Gombe.