fbpx
Thursday, February 9
Shadow

Ba kora ta Ganduje yai ba, ‘wannan ƙarya ce mai gishiri’, in ji Baba Impossible

Tsohon Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Kano, Muhammad Tahar Adam, wanda aka fi sani da Baba Impossible, ya ce shi ya ajiye muƙamin da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bashi a raɗin kan sa.

Da ya ke magana a Freedom Radio a yau Asabar, Baba Impossible ya bayyana cewa tun a jiya Juma’a ya rubuta takardar ajiye aiki ya kuma kai wa Sakataren Gwamnati, Alhaji Usman Alhaji da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamna, Usman Bala, kwafin na gwamna kuma su ka buga masa stamfi.

A cewar Baba Impossible, bayan ya kai takardar, abin mamaki kawai sai ya ga an fitar da sanarwa cewa wai Gwamna ya kore shi sabo da ya na aikata abubuwa marasa kyau kuma ba ya biyayya ga Gwamna.

Karanta wannan  Ku Cigaba Da Kashe Tsoffin Kudadenku, Idan Ma An Daina Karba Ni Da Kaina Zan Kai Muku Banki A Canja Muku Su Da Sabbin Kudi, Kiran Gwamna Elrufai Ga Al'ummar Jiharsa Ta Kaduna

“Wannan abin mamaki ne sabo da ni a gani na, cikakkiyar gwamnati ba za ta yi karya ba. Wannan ƙarya ce mai gishiri.

“Bayan na riga na kai takardun murabus di na kuma an karɓa sannan kuma wani ya fito ya ce wai an kore ni.

“To wannan magana an rufe ta kuma mun bari, amma idan sun ci gaba za ku ci gaba,” in ji Baba Impossible.

Daily Nigerian.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *