fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Ba ku tausayin talakawan kasar nan – Kungiyar Yan Kasuwa (TUC) ta yi tir da shirin Gwamnatin Tarayya na kara farashin man fetur

Kungiyar yan kasuwa (TUC) ta ce shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yanke na kara farashin Man Fetur ya nuna cewa ba ta tausayin talakawa a kasar nan.

Dangane da bayanin da Sylva ya yi, TUC, a cikin wata sanarwa mai taken ‘Me ya sa kake saurin gaya mana game da hauhawar farashin danyen mai?’ Ya ce shirin da ake yi na karin farashin man fetur yana nuna cewa gwamnati ba ta jin tausayin talakawa.

TUC ta ce da alama gwamnatin ba ta damu da halin talaucin da ‘yan Nijeriya ke fama da shi ba da kuma rashin aikin yi da rashin tsaro da sauransu.

A karshe kungiyar tayi Kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sauya tunanin ta kan karin farashin man fetur a kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *