fbpx
Friday, July 1
Shadow

“Ba kudi ne yasa Atiku yayi nasarar lashe zaben fidda gwani ba”>>Sule Lamido

Tsohon gwaamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya bayyana cewa da ace kudi aka amfani dashi wurin yin zaben fidda gwani na PDP, to da Atiku ba zai doke gwamna Wike ba.

Sule Lamido ya bayyana hakan ne a talabijin din Channels yayin suke ganawa dashi ranar laraba kan maganar zaben fidda gwanin na PDP.

Inda ya kara da cewa addu’o’i ne suka taikamawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yayi nasara akan gwamnan Rivers, Nyesom Wike amma ba sayen deliget ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.