fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Ba mu da makiyin da ya kai ka – IPOB ta mayarwa Wike martani

Yan asalin Biafra, IPOB, a jiya, sun mayar da martani ga Gwamnan Jihar Ribas, Gwamna Nyesom Wike, inda suka ce shi ne mafi sharri daga cikin makiyan Biafra da IPOB.

Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ta yi zargin cewa Gwamna Wike yana da takaitaccen tunani, inda ta kara da cewa furucin da ya yi a baya-bayan nan cewa shi (Wike) na goyon bayan kungiyar IPOB bayan ya ayyana su a matsayin masu tayar da kayar baya alama ce da ke nuna cewa munafiki ne mai baki biyu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar IPOB, Emma Powerful, ya fitar mai taken ‘Gwamna Nyesom Ezenwo Wike ya fi dukkan makiyan Biafra da IPOB sharri’, yace kungiyar ta yi mamakin, inda tace kamar ba gwamnan jihar Ribas Wike ba ne, wanda ya ayyana kungiyar ta IPOB a matsayin kungiyar masu tayar da kayar baya tare da bayar da umarnin mambobinta su nisanta kansu daga jihar Ribas.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: La Liga ta kai karan PSG wurin hukumar wasan kwallon kafa ta UEFA bayan Mbappe ya fasa komawa Madrid

Kungiyar ta kara da cewa idan har yana so ta amince yana goyon bayan ta, sai taimaka wajen kubutar da mambobin kungiyar da akayi garkuwa da su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.