fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Ba mutunci zan yi maganin Oshiomhole>>Obaseki

Gwamnan jihar Edo,  Godwin Obaseki yayi magana bayan lashe zaben da yayi a karo na biyu inda yace muddin tsohon uban gidansa, Adams Oshiomhole bai canja abinda yake ba to zai dandana kudarsa.

 

Obaseki ya bayyana hakane a ganawa ta musamman da yayi da gidan talabijin din Arise inda aka tambayeshi ka  rade-radin dake yawo cewa wai zai kori Oshiomhole daga jihar.

Yace wannan ba gaskiya bane amma idan Oshiomholen be kama girmansa ba ya ci gaba da daukar nauyin wasu suna abinda bashi kenan ba to zai dandana kudarsa dan zai rufe ido yayi maganinsa.

Karanta wannan  Tinubu zai yi nasara da kashi 60 cikin 100 a zaben 2023 – Okechukwu

 

Da yake Magana akan Tinubu da irin rawar da ya taka a kan maganar sake zaben sa, yace Tinubu da Oshiomhole suna da wata halayya wadda suke so su rikawa mutane karfa-karfa amma maganar gaskiya itace idan basu canja ba dolene a taka musu birki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.