Taurarin fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya bayyana cewa bashine ya zagi shugaban kasa, Muhammadu Buhari ds matarsa, A’isha ba.
A wani bayani da Adamun yayi da kakkausar murya ya bayyana cewa shi dan kasane na gari kuma baya zagin shuwagabanni saidai ya bada shawara.
Yace amma an samu wani “Tsinanne” a shafin Twitter da yake amfani da sunansa yana zagin shugaban kasa da matarsa, Adamu ya kara da cewa bashi bane.