fbpx
Friday, August 12
Shadow

Ba tsinannun fastoci bane suka halacci taron kaddamar da Kashim Shettima, cewar kungiyar kamfe ta Tinubu

Kingiyar dake yiwa dan takarar shugaban kasa na APC Tinubu yakin neman zabe tace ba fastocin boge ne suka halacci taron kaddamar da Kashim Shettima ba.

A ranar laraba Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na zaben shugaban kasa.

Kuma Kiristoci na kalubalantar fastocin da suka halacci taron ganin cewa APC ta ware su ta tsayar da Musulmai a matsayin ‘yan takararta, inda har wasu suka ce fastocin tsinannu ne kuma na bogi ne.

Amma yanzu kungiyar dake yiwa Tinubu yakin neman zabe tace ba tsinannu fastoci ne suka halacci taton ba, shuwagabannin Kirista ne na gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published.