fbpx
Tuesday, December 1
Shadow

Ba za a iya samun sahihin zabe ba tare da inganta dokokin zabe ba>>PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Juma’a ta ce zabuka a Najeriya ba za su kasance masu inganci ba har sai an inganta dokokin zaben a kasarnan.

 

Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Mista Kola Ologbondiyan, ya bayyana hakan a Abuja a wani taron manema labarai kan kudurorin jam’iyyar daga taron kwamitin zartarwa na kasa na 90 na ranar Alhamis.

 

Ologbondiyan ya ce jam’iyyar ta yanke shawarar kafa wani babban kwamiti wanda zai yi aiki tare da Majalisar Dokoki ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki kan gyaran Dokar Zabe don yin zabukan Najeriya a cikin gaskiya da amana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *