Ba za a sa wa Trump ankwa ba idan ya je kotu in ji lauya
Lauyan tsohon shugaban Amurka ya ce ba za a sanya wa Donald Trump ankwa ba, idan ya halarci zaman kotu a New York a makon gobe.
An tambaye shi ne a gidan talbijin na ABC News ko yaya yake zaton tsarin gurfanar da Trump gaban kotu zai kasance, Joe Tacopina ya ce ya “tabbata [masu shigar da ƙara] za su yi ƙoƙarin samun duk wani ɗigo na jan hankalin jama’a da za su iya, a kan wannan abu.
Amma ya ƙara cewa ba za a sa wa shugaban ankwa ba”.
Tun farko rahotanni sun tabbatar da Za a iya kama Donald Trump nan da ƴan kwanaki. Lauyan Trump ya ce: “Na fahimci cewa za su rufe hanyoyin zuwa yankin da ke zagaye da kotun, idan an zo gurfanar da shi, kuma su rufe ginin kotun.
“Za mu je can… kuma mu ce ba a aikata laifi ba, za a fara magana ne game da hanyar shigar ƙararrakin, abin da za mu yi kenan nan take kuma ba tare da ƙaƙƙautawa ba, dangane da dacewar wannan ƙara ta fuskar shari’a.”
Kotu a birnin New York ce ta tuhumi tsohon shugaban ƙasar Donald Trump da hannu kan zargin biyan kuɗi domin ɓoye alaƙar da ke tsakaninsa da wata mai fina-finan batsa.
Ana zargin Trump ne da biyan kuɗi ga matar mai suna Stormy Daniels gabanin zaɓen 2016 domin ta rufe baki kan alaƙar da ta wanzu tsakaninsu.