Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta ce ba za ta sake kai kayan zaɓe masu muhimmanci ajiya ba a Babban Bankin Najeriya (CBN).
Da yake magana yayin wani taron ƙara wa juna sani a Abuja ranar Asabar, shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya ce daga yanzu CBN ba zai sake ajiye kayan zaɓen ba tun daga kan zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da za a yi ranar 18 ga watan Yuni.
Bisa al’ada, INEC kan kai kayan zaɓe kamar takardun jefa ƙuri’a da takardun rubuta sakamako da abin jefa ƙuri’a na masu lalurar ido ajiya a CBN kafin fara kaɗa ƙuri’ar yayin zaɓuka a Najeriya.
Sai dai babu tabbas ko matakin na da alaƙa da ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan rahotannin da ke cewa Gwamnan CBN Godwin Emefiele na son ya nemi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar – kodayake ya musanta batun.
Ya ce: “Muna duba yadda za mu inganta gudanar da ayyukan, saboda haka ba lallai ne hakan yana da alaƙa da abin da ke faruwa a CBN ba. Manufarmu ita ce a kodayaushe mu inganta da kuma gudanar da ayyukanmu da kanmu.
“Ba za mu yi amfani da CBN ba a zaɓen Ekiti, za a kai kayan zaɓen daga ofishinmu na Abuja zuwa filin jirgi sannan a kai su ofishinmu na jiha.”