Thursday, July 18
Shadow

Ba za mu taɓa yin sulhu da ‘yan bindiga ba – Gwamnan Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na rashin yin sulhu da ‘yan bindiga.

Yayin da yake gabatar da jawabi bayan ya shiga wani tattaki da ƙungiyoyin matasan jihar suka shirya a wani ɓangare na bikin ranar Dimokradiyya, Gwamnan Dauda ya ce zai yi duk abin da ya dace domin maido da jihar kan turbar zaman lafiya.

”Jiharmu na da tarihin zaman lafiya, amma sannu a hankali abubuwa suka fara taɓarɓarewa, sakamakon ayyukan ɓata-gari”, inji gwamnan.

Gwamnan ya ce matsalar tsaro matsala ce da ta shafi kowa da kowa, don haka ya yi kira ga al’ummar jihar su haɗa hannu wajen tabbatar da zaman lafiyar jihar.

Karanta Wannan  Hotuna: An kamasu sun sàci mota a masallacin Abuja

“A koyaushe ina faɗa ina maimaitawa bai kamata ka yi sulhu da kasasshe ba, mun ga yadda gwamnatocin da suka gabata suka yi yunƙurin sulhu da ‘yan bindigar nan, amma babu abin da hakan ya haifin sai ƙara wa ‘yan fashin suna, don haka ne a yanzu muka ɗauki matakin ba za mu taɓa yin sulhu da kowane ɗan bindiga ba”, in ji gwamnan na Zamfara.

Ba Gwamnan Zamfara ba ne kawai ya ce ba zai yi sulhu da ‘yan bindiga ba, akwai gwamnonin jihohin arewacin ƙasar da dama da suka ce ba za su yi sulhu da ‘yan bindigar ba.

Karanta Wannan  DAMBARWAR MASARAUTAR KANO: Lauyoyin Sarki Aminu Ado Bayero Sun Janye Daga Tsaya Masa

Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin arewacin ƙasar da ke fama da matsalar ‘yan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *