Hukumar dake shirya bayar da kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Duniya, Ballon d’Or, watau mujallar France Football ta bayyana cewa a bana ba za’a bayar da kyautar ba.
Tace saboda yanda shekarar tazo aka tsayar da wasanni kuma aka dawo da buga wasannin ba tare da ‘yan kallo ba sannan gasar Ligue 1 aka soke ta, da wuya ayi adalci idan aka ce za’a bada kyautar ta bana, cewar Editan Mujallar, Pascal Ferre.
Wannan ne karin farko da ba’a bayar da kyautar ba tun bayan fara bayar da ita a shekarar 1956. Dan kwallon kasar Argentina me bugawa Barcelona wasa, Lionel Messi ne wanda yafi yawan kyautar inda yake da guda 6, sai babban abokin takararshi, Cristiano Ronaldo dake take masa baya da guda 5.
Saidai yace za’a yi zaben kungiyar gwanayen ‘yan kwallo ta duniya watau Best XI