fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Ba za’a canja hukuncin da aka yankewa wanda yayi kalaman batanci ga Annabi ba>>Gwamnatin Kano tawa Majalisar Dinkin Duniya martani

Gwamnatin Kano ta ce ba za ta sauya matsayinta ko na kotun shari’a ba, kan hukuncin da aka yankewa yaron nan Omar Faruk kan laifin kalaman ɓatanci kan annabi, tare da cewa shekarun sa 16.

Asusun kula da ilimin kananan yara na Unicef ya bukaci gwamnatin tarayya ta taka rawa wajen ganin gwamnatin Kano ta gaggauta janye hukunci da sake nazarin shari’ar da ta yi wa yaron mai shekara 13.

A ranar 10 ga watan Agusta ne wata kotun shari’ar musulunci a jihar Kano ta yanke hukuncin shekara 10 kan yaron da aiki mai sassauci.

Karanta wannan  Ji bayani dalla-dalla yanda 'yan Bindiga suka kaiwa tawagar motocin shugaba Buhari hari

Unicef a wata sanarwar da ta fitar a ranar Laraba a Abuja ta ce hukuncin ya ci karo da dokokinta na kare haƙƙin yara na 1991, da Najeriya ta aminta da shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.