Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu ya bayyana cewa, ba zai yiyu a fitar da dan takara daya tilo ba tare da zaben fidda gwani ba a jam’iyyar.
Yace zaben dan takarar shugaban kasa ba irin na shugaban jam’iyya bane wanda aka zabeshi a matsayin wanda zai zama shugaban ta ba tare da zabeba.
Yace akwai ‘yan takara da yawa da suka sayi fom kuma kowane na da dama, doka ta bashi damar sayen fom dan haka ba zaka hanasu ba.
Yace amma sun san cewa mutum da yane Allah zai zaba ya baiwa wannan kujera.