Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari a jiya ranar sati yayin dayake yakin neman zabe a kudancin kasar nan.
Yayin daya bayyana cewa ba zai yiyu gwamnati ta kira matasa malalata ba alhalin bata bayar da ingantacciyar wutar lantarki ba.
Inda ya kara da cewa Najeriya nada albarka sosai da har zata iya samarwa kanta wutar lantarki kuma ta baiwa wasu kasashe a nahiyar turai.
Shekaru hudu baya ne shugaba Buhari ya kira matasan Najeriya malalata a wani taron da suka gudanar na shuwagabanni a Ingila, yayin da Tinubu ya bashe amsar maganar tashi a jiya inda yake yakin neman zabe.