fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Ba zai yiyu mu je mu yiwa ‘yan Bindiga ruwan bamabamai ba>>Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da yasa ba zai yiyu ta yiwa ‘yan Bindiga ruwan bamabamai ba.

 

Tace idan ta yi hakan, za’a kashe wanda babu ruwansu wanda hakan ba daidai bane.

 

Ministan yada labarai,  Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana haka yayin ganawa da wani gidan rediyo a Legas me suna Bond FM ranar Asabar kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya,  NAN ya ruwaito.

 

Lai Muhammad yace ba zai yiyu a nuna karfi a yiwa ‘yan Bindigar ruwan bamabamai ba idan kuwa ba haka ba, lallai za’a kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba dake zaune a kusa da inda suke zaune.

 

Saidai yace gwamnatin tarayya bata yi kasa a gwiwa ba wajan samarwa da jami’an tsaron Najeriya makamai masu inganci ba, kuma duka sauran jami’an tsaron an samar musu da kayan aiki masu kyau yanda zasu iyayin aiki tare da sojoji.

 

Yace hakanan suna baiwa kula da ‘yansandan Najeriya muhimmanci sosai,  yace kwanannan ne ma suka dauki karin ‘yansanda 25,000 inda aka kaisu jihohinsu na Asali dan samar da tsaro.

Karanta wannan  Mun nunawa Abba Gida-Gida Soyayya amma ya nuna mana kiyayya>>Inji Wani da aka rushewa shago a Kano

 

“We cannot just go with full force to bomb them or else the innocents living around them will be killed, and we don’t want that to happen,” he said.

 

“We have been trying our best in the fight against the bandits by equipping all our security apparatus; the government has purchased aircraft so that they can fight alongside the soldiers. We have not rested on our oars.

 

“The welfare of the police is also given adequate attention, and very recently, this administration recruited 25,000 constables and deployed them to their home states. This will go a long way in community policing,” the minister said.

(NAN)

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *