fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

“Ba zaka iya mulkar Najeriya a shekarar 2023 ba, ka bari sai 2027 ko 2031”>>Babangida ya fadawa Peter Obi

Tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu ya bayyanawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi cewa ba zai iya mulkar Nijeriya a shekarar 2023 ba.

Inda yace yayi gaggawa kamata yayi ya bari sai a shekarar 2027 ko kuma shekarar 2031 sai ya nemi takarar shugaban kasar.

Babangida ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai na Channels, kuma yace masu Obi mutun ne na gari.

A karshe Babangida yace da ace Peter Obi bai sauya sheka ba da shi Atiku zai zaba a matsayin abokin takararsa a jam’iyyar PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published.