Kungiyar Ohanaeze Indigbo dake kare muradun Inyamurai ta caccaki Atiku kan lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP.
Ohanaeze Indigbo ta bayyana hakane ta bakin wakilinta, Mazi Okechukwu Isiguzoro inda yace ba zasu zabi Atiku ba.
Tace sam ba’a yi adalci a cikin zaben fidda gwanin ba kuma an zalinci yankinsu na Inyamurai.
Dan haka tace ba zasu zabi Atiku ba kuma ba zai ci zaben shekarar 2023 ba.