Deborah daliba ce a makarantar koyarwa ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, dalibar an zargeta da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
CAN ta ce “Mun shirya Zanga-zangar Allah wadai da Kisan ‘yar mu Deborah Yakubu, za muyi taron ne a duk sakatariyar mu ta jihohi, Jihar da bamu da Sakatariya, zamu yi taron a babbar Majami’ar dake Jihar.
Mun yanke shawarar yin Zanga-zangar ne a cibiyoyinmu da majami’unmu ba akan tituna ba, saboda kaucewa sake rasa wasu rayukan da kaucewa tarzoma.
A ranar Jumu’a a ne wata jarida ta ruwaito cewa, wata Daliba a makarantar koyarwa ta Shehu Shagari, Deborah Yakubu da aka zargeta da batanci ga Annabi Muhammad (SAW), hakan ya jawo fusatattun matasa suka kwace ta daga hannun jami’an tsaro suka mata duka, wanda hakan ya yi ajalinta nan take.
Daga Leadership.