Shahararren marubuci, Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa ya karanta sakon Bishop Matthew Kuka na ranar Kirsimeti amma bai ga inda Malamin Kiristan ya ci zarafin Musulunci ba.
Soyinka ya bayyana hakane a sakon da ya fitar akan martanin da Jawabin Bishop Kuka ya rika samu inda wata kungiyar Musulmai dake Sokoto ta nemi ya bada hakuri kan kalaman ko kuma ya bar Sokoto.
Soyinka yace wannan barazana ba abune da za’a amince dashi ba inda yace Najeriya kasa ce ta kowa da kowa ba ta wani bangare ko addini ba.
Kasancewar Soyinka wanda ke addinin gargajiya, yace za’a iya cewa bashi hurumin yin magana akan lamarin amma a matsayinshi na dan kasa yana da damar magana akan lamarin ds ya shafi kowa da kowa.