Gwamnatin kasar Ingila ta bayyana cewa, ba zata baiwa haramtacciyar kungiyar dake son kafa kasar Biafra ta IPOB mafakar siyasa ba.
Ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta saka IPOB cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda sannan kuma ta samu Rahoton yanda kungiyar ke take hakkin bil’adama.
Tace ita da kungiyar MASSOB da duk wani sake da alaka dasu ba zata basu damar mafakar siyasa ba.